logo

HAUSA

Kuri'ar jin ra'ayi ta CGTN: Fiye da 90% na masu amfani da yanar gizo sun yi suka ga 'yan siyasar Amurka kan girman kai da jahilci

2024-02-03 19:46:06 CMG Hausa

A ranar 31 ga watan Janairu, a zaman da aka yi a birnin Washington, dan majalisar dattawan Amurka na kwamitin shari’a na majalisar, Tom Cotton ya yi jerin “tambayoyi” na jahilci ga shugaban kamfanin TikTok Shou Zi Chew, inda ya yi masa tambaya ko yana da shaidar zama dan kasar Sin, ko ya taba shiga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da dai sauransu. Shirmen da ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi a zaman taron ya zama abin tattaunawa tsakanin mutane a yanar gizo a fadin duniya. 

Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a na masu amfani da yanar gizo a duniya da CGTN ya fitar, ya nuna sama da kashi 90.7 cikin 100 na masu amfani da yanar gizo sun yi imanin cewa, tambayoyin da wasu 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi sun fallasa jahilci, girman kai, da kyamarsu ga kasar Sin, wanda a karshe zai kawo cikas ga ci gaban dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka. (Yahaya)