logo

HAUSA

Kasancewa tare da jama'a: Al'adar Xi Jinping a lokacin bikin sabuwar shekara

2024-02-03 15:28:58 CMG Hausa

A wani gidan gona na wani kauye a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, kayan lambu da 'ya'yan itatuwa na jiran a debo su a tafi da su. An kintsa wasu wanda za a ajiye a teburin cin abinci na mutanen wurare daban daban.

Wannan kauye sunansa Diliubu, wanda aka fi sani da babban tushen kayan lambu na biranen Beijing da Tianjin na kasar Sin, zai samar da kayayyakin amfanin gona ga manyan biranen kasar a lokacin bikin bazara dake tafe, ko kuma bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.

A yayin da kauyen ya kasance zangon farko na rangadin kwanaki biyu da ya yi a birnin Tianjin, shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Alhamis ya ziyarci kauyukan da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a lokacin zafin da ya gabata, ya kuma samu labarin farfadowar ayyukan noman a yankin.

Shekaru da dama, shugaba Xi na kasar Sin yana da al'adar ziyartar talakawa, musamman ma marasa galihu, gabanin bikin bazara, hutu mafi muhimmanci a kalandar kasar Sin, wanda ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekara, bikin wani lokaci da ake kasancewa tare da iyali a bisa al’ada. (Yahaya)