logo

HAUSA

Sin Ta Gabatar Da Taswirar Raya Kauyuka Cikin Takarda Mai Lamba 1 Ta Kwamitin Tsakiya Ta 2024

2024-02-03 20:17:33 CGTN HAUSA

DAGA CGTN HAUSA

Yau Asabar, an gabatar da takarda mai lamba 1 wadda ke da nasaba da aikin jagorar ayyukan raya kauyuka da manoma da aikin gona, kuma ta kasance irinta karo na 12 bayan an kammla babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18.

Wannan takarda mai taken “Shawarar raya kauyuka a dukkan fannoni bisa dabaru masu amfani na shirin ‘Kafa kauyuka fiye da dubu na misali da yiwa kauyuka kwaskwarima’ na majalisar gudanarwa da kwamitin kolin JKS”. Takarda ya kasu kashi 6, wato tabbatar da samar da isasshen hatsi, da hana mutane sake fama da talauci, da daga matsayin raya sana’o’in kauyuka, da kuma daga ingancin raya da daidaita harkokin kauyuka, kana da kara karfin JKS na jagorantar ayyukan raya kauyuka da manoma da aikin gona. (Amina Xu)