logo

HAUSA

Xi ya ziyarci sojojin da aka jibge a Tianjin

2024-02-03 19:58:48 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci sojojin da aka jibge a birnin Tianjin dake arewacin kaasr Sin gabanin bikin bazarar ko sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kwamitin sojin kasar, ya mika gaisuwar bikin ga rundunar 'yantar da jama'a da na rundunar 'yan sandan kasar, da fararen hula da ke aiki tare da sojoji, da ‘yan sa kai da na dakarun kiyaye zaman lafiya, a madadin kwamitin koli na JKS da kwamitin sojin kasar. (Yahaya)