logo

HAUSA

Kamfanonin kasar Sin sun ba da gudummawar kayayyakin yaki da cutar kwalara ga kasar Zimbabwe

2024-02-03 15:34:29 CMG Hausa

A ranar Juma'a ne kamfanonin kasar Sin dake kasar Zimbabwe suka ba da gudummawar kayayyakin yaki da cutar kwalara da darajarsu ta kai dalar Amurka 10,000 ga kasar ta Zimbabwe

Hukumomin kasar Sin dake karkashin rukunin kamfanonin kasar Sin dake Zimbabwe (CCEZ) sun kai kayayyakin da suka hada da maganin kashe kwayoyin cuta, da tufafin kariya, da tantuna da kayayyakin abinci zuwa asibitin cututtuka masu yaduwa dake hanyar Beatrice dake birnin Harare.

Gideon Mapokotera, jami'in kula da albarkatun jama'a na lardi a ma'aikatar lafiya da kula da yara ta kasar Zimbabwe, ya godewa kamfanonin kasar Sin bisa gudummawar da suka bayar, yana mai kallon ta a matsayin babban taimako wajen yaki da cutar kwalara.

Jami'in na kasar Zimbabwe ya kara da cewa, "Sinawa sun kasance abokai na kwarai a kullum a kasar Zimbabwe. Sun kawo kayayyaki iri-iri...kuma wadannan za su taimaka matuka wajen karfafa gwiwar ma'aikatanmu, da kuma taimakawa al'ummarmu." (Yahaya)