logo

HAUSA

Sin za ta horas da jami’an gwamnatin Sudan ta Kudu dabarun kara kwarewar aiki a shekarar 2024

2024-02-02 09:51:01 CMG Hausa

Jakadan Sin a Sudan ta Kudu, Ma Qiang ya bayyana cewa, kasarsa za ta dauki nauyin horar da jami'an kasar Sudan ta Kudu kwasa-kwasai har guda shida a shekarar 2024, kan raya albarkatun jama’a.

Jakada Ma ya bayyana yayin wani biki da aka gudanar a ofishin jakadancin kasar Sin dake Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu cewa, a bana, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannin raya albarkatun jama'a tare da Sudan ta Kudu, baya ga shirya kwasa-kwasan horaswa guda shida ga Sudan ta Kudu a kasar Sin, wadanda suka shafi aikin gona,da ilimi, da kasuwanci, da sufuri, da man fetur da sauransu.

A shekarar 2023, sama da jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu da kwararru da ma'aikatan fasaha 300 ne, suka halarci shirye-shiryen samun horo na gajeren lokaci a kasar Sin, wadanda suka shafi fannonin tattalin arziki, da kasuwanci, da aikin gona,da ilimi, da kiwon lafiya, da kuma fasaha.

A jawabinta, ministar kula da harkokin majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu, Mary Nawai Martin, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar kwasa-kwasan horarwa a kasar Sin, ta bayyana cewa, gwamnatin Sudan ta Kudu tana godiya ga fasahohin da gwamnatin kasar Sin ta samar musu.

Ta kuma yi nuni da cewa, Sudan ta Kudu na da burin karbar karin masu zuba jari na kasar Sin, domin taimakawa kasar wajen raya kasa, a daidai lokacin da kasar ta sauya daga shekaru da ta shafe tana fama da tashin hankali, zuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Ibrahim)