logo

HAUSA

Kenya ta kaddamar da shirye-shiryen janyo hankalin masu yawon bude ido daga yammacin Afirka

2024-02-02 11:03:10 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta kasar Kenya (KTB), ta bayyana a jiya Alhamis cewa, tana da burin kara yawan masu yawon bude ido dake zuwa kasar daga kasashen yammacin Afirka, ta hanyar inganta harkokin kasuwanci da na shakatawa a kasar.

A yayin wani taron da aka shirya don fara aiwatar da jerin gwanon gangamin wayar da kan jama’a a kasashen Najeriya da Ghana, mukaddashin babban jami'in gudanarwa na hukumar KTB, John Chirchir, ya bayyana muhimmiyar rawar da kasuwannin yammacin Afirka ke takawa a fannin dabarun fadada kasuwannin yawon bude ido da kuma bangarorin da Kenya take fatan nufa.

Chirchir ya ce, kasashen Najeriya da Ghana sun samu ci gaba a fannin yawon bude ido, inda aka samu karuwar kashi 6 da kashi 48 cikin 100 a shekarar 2023.

Hukumar yawon bude ido ta Kenya (KTB) da kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar wato Kenya Airways ne ke jagorantar sama da kamfanonin tafiye-tafiye 15, don gudanar da ayyukan raya kasuwanci da aka shirya yi daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Fabrairu a garuruwa daban-daban na kasashen Najeriya da Ghana, inda ake sa ran za su jawo hankalin abokan ciniki sama da 400. (Ibrahim)