logo

HAUSA

Ma’aunin cinikayyar ba da hidimomi ta kasar Sin ya kai sabon matsayi a tarihi

2024-02-02 13:45:43 CMG Hausa

Alkaluman da hukumar cinikayyar kasar Sin ta fitar a jiya Alhamis na nuna cewa, a shekarar bara, cinikayyar ba da hidima ta kasar Sin ta karu sannu a hankali, inda ma’aunin ya kai wani matsayi a tarihi. Haka kuma cinikayar dake bukatar hidimar ilimi ko kwararru ta karu cikin sauri, wanda ya zama sabon karfi na ci gaban cinikayyar ba da hidima.

Alkaluman da ma’aikatar cinikayya ta fitar a jiya Alhamis na cewa, a shekarar bara, darajar shige da ficen cinikayyar ba da hidimomi ta kasar Sin ta kai kudin Sin RMB yuan fiye da triliyan 6.5, wanda ya karu da kashi 10 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.

A halin yanzu, kasar Sin tana da sansanonin fitar da kayayyaki na musamman guda 112, wadanda suka shafi fannoni guda 7 kamar al’adu,hidimomin zamani, da bayanan labarin kasa, da ’yancin mallakar fasaha da hidimomin harsuna. (Safiyah Ma)