logo

HAUSA

Kungiyar Houthi ta kaiwa jirgin ruwan kasuwanci na Burtaniya hari a Bahar Maliya

2024-02-02 11:01:43 CMG Hausa

Kakakin kungiyar Houthi ta Yemen, Yahya Saraya ya bayar da sanarwa a jiya Alhamis cewa, kungiyar ta harba makamai masu linzami kan wani jirgin ruwan kasuwanci na Burtaniya dake tafiya a tekun Bahar Rum a wannan rana, don hana shi zuwa tashar jiragen ruwa na Isra'ila.

Ofishin kula da harkokin kasuwancin teku na Burtaniya, ya sanar jiya Alhamis cewa, wani jirgin ruwan fatauci ya ba da rahoton fashewar wani abu a cikin teku a kusa da gefen jirgin ruwa a tazarar kilomita 57 daga yammacin birnin Hodeida na gabar tekun Yemen da tsakar rana. Sai dai fashewar ba ta haifar da barna a cikin jirgin ba kuma babu wanda ya samu rauni a cikin jirgin.

Tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Falasdinu da Isra’ila a watan Oktoba na shekarar bara, dakarun Houthi ta Yemen suka yi amfani da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami, wajen kai hare-hare kan jiragen ruwa a cikin Bahar Maliya. Tun daga ranar 12 ga watan Janairu na bana, Amurka da Burtaniya sun kai hare-hare ta sama kan kungiyar Houthi ta Yemen a jere, wadanda suka haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama. Wasu kasashe sun yi Allah wadai da matakin da Amurka da Burtaniya suka dauka, suna ganin cewa, hakan cin zarafi ne ga kasar Yemen, kuma zai tsananta halin da ake ciki a yankin. (Safiyah Ma)