logo

HAUSA

Xi zai yi aiki tare da Trong don inganta al'ummar Sin da Vietnam mai makomar bai daya

2024-02-02 19:35:59 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Juma’a cewa, a shirye yake ya yi aiki tare da bangaren Vietnam, wajen sa kaimi ga gina al'ummar Sin da Vietnam mai makomar bai daya don samun nasarori masu kyau.

Xi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar taya murna da musanyar gaisuwar bikin bazara da Nguyen Phu Trong, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam. (Yahaya)