logo

HAUSA

Sojojin Isra'ila sun sako Falasdinawa 114 da suka kama a wani samame da suka kai a Gaza

2024-02-02 10:41:33 CMG Hausa

Sojojin Isra'ila sun sako Falasdinawa 114 ta mashigar Kerem Shalom da ke kudancin zirin Gaza, wadanda aka kama a yayin samame ta kasa da suka kai zirin.

Majiyar tsaron Falasdinu a hukumar dake kula da kan iyaka a Gaza, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kai wasu daga cikin Falasdinawan da aka sako zuwa asibitin Najjar da ke birnin Rafah, saboda tabarbarewar yanayin lafiyarsu.

A yayin farmakin da sojojin Isra'ila suka kai ta kasa a zirin Gaza, sun kame daruruwan Falasdinawa tare da kai su wasu wuraren da ba a sani ba, kamar yadda Euro-Med Human Rights Monitor ta bayyana.

Wasu daga cikin fursunonin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya gana da su a lokacin da suke asibiti, sun ce an yi musu duka, an wulakanta su, tare da azabtar da su a lokacin da ake tsare da su, zargin da ba a tantance ba.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a jiya Alhamis cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a zirin Gaza, ya zarce dubu 27. (Ibrahim)