logo

HAUSA

AMIC ta samu kudin shiga matuka bisa rikici da yake-yake

2024-02-01 20:01:31 CMG HAUSA

Majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta gabatar da wani rahoto, wanda ya jawo hankalin kasa da kasa, rahoton ya ce, yawan kudin da Amurka ta samu daga sayar da makamai ga kasashen ketare ya karu da kashi 16% a shekarar 2023, wanda ya kai dala biliyan 238. Daga cikinsu, gwamnatin ta samu dala biliyan 80.9 daga shawarwari da ta yi kai tsaye wajen sayar da makamai, wanda ya karu da kashi 56% bisa na shekarar 2022, ban da wannan kuma, yawan makaman da kamfanoni masu zaman kansu suka sayar ya kai dalar biliyan 157.5, wanda ya karu da kashi 2.5% bisa na shekarar 2022.

A shekarar 2023, Amurka ta samun kudin shiga mai dimbin yawa a wannan fanni, saboda ganin cewa, a wani bangare, ana ci gaba da rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine, har ma an sake tada zaune tsaye a yankin Palasdinu da Isra’ila, rikice-rikicen da su barkewa bi da bi a duniya na tsananta halin tsaro a duniya, abin da ya ingiza kasashe da dama ke sayan karin makamai. A wani bangare kuma, Amurka na amfani da wannan dama don gwada makaman da ta kera, matakin da ya ingiza fasaharta wajen kera makamai, yayin da ta mamaye wannan kasuwa.

Rikici da yake-yake, sun kawowa fararen hula matukar barazana da bacin rai, amma sun baiwa rukunin masana’antun samar da makamai na Amurka da aka fi sani da AMIC damar samun karin kudin shiga mai yawan gaske. (Amina Xu)