logo

HAUSA

'Yan sandan Sin sun kama tan 25.9 na miyagun kwayoyi a shekarar 2023

2024-02-01 10:02:33 CMG Hausa

Ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shekarar 2023, 'yan sandan kasar sun gudanar da bincike tare da daidaita manyan laifukan da suka shafi migayun kwayoyi fiye da dubu 42 tare da kame fiye da mutane dubu 65 da ake zargi, da kuma kama tan 25.9 na miyagun kwayoyi.

Rahotanni na cewa, 'yan sanda a fadin kasar Sin sun daidaita laifuffuka sama da 200 da suka shafi samar da miyagun kwayoyi a shekarar 2023, inda suka kama fiye da tan 740 na kayayyakin da aka yi amfani da su wajen samar da miyagun kwayoyi.

A cewar ma’aikatar, hukumomin tsaron jama’a a fadin kasar sun karfafa sanya ido kan shaye-shayen miyagun kwayoyi tare da duba yadda ake ta’ammali da miyagun kwayoyi a cikin shekarar da ta gabata.