logo

HAUSA

Gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun himmatu wajen kaddamar da rundunar tsaron sa kai a jihohinsu

2024-02-01 09:24:21 CMG Hausa

An kaddamar da rundunar jami’an tsaron al’umma na sa kai a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya domin su taimakawa hukumomin tsaron gwamnati wajen kare al’umma daga barazanar ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Adadin matasa 2,645 ne aka kaddamar da aikinsu daga cikin mutum 5,200 da gwamnatin jihar ta yi hasashen za ta dauka domin gudanar da wannan aiki a yankunan kananan hukumomi 14 dake jihar, kuma dukkansu sun samu horo na kwarewar aiki sosai daga hukumomin tsaron Najeriya daban daban.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

An kaddamar da dakarun ne da ake yiwa lakabi da Askarawan Zamfara a katafaren filin baje koli dake Gusau, fadar gwamnatin jihar a wani bikin da ya samu halartar gwamnonin jihohin Jigawa da Kano da Kebbi da Kaduna da Katsina da kuma Sokoto.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, gwamnan jihar ta Zamfara Alhaji Dauda Lawan ya ce, kaddamar da dakarun tsaron al’umma daya ne daga cikin matakan da yake dauka wajen samar da natsuwa da kwanciyar hankali a zukatan al’ummar jihar da kuma sauran ’yan kasuwa na gida da na waje masu sha’awar zuba jari a jihar ta Zamfara.

“Kamar yadda muka fada, maganar tsaro ta shafi kowa da kowa, ba maganar jam’iyyar ba ne. Abu ne ya zama ruwan dare gama duniya, da mu da Sokoto da Kebbi da Katsina da Kaduna da Jigawa da Kano duk abu daya ne, sabo da haka muna kira da ku ba mu hadin kai.”

Shi ma a jawabinsa gwamnan jihar Katsina, kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Dikko Radda ya tabbatar da cewa, dukkannin gwamnonin sun amince da murya guda kan cewa babu wani zaman sulhu da za su yi da ’yan bindiga, sakamakon cewa sun riga sun dauki dukkan matakai da suka kamata wajen ganin an sami dauwamammen zaman lafiya a shiyyar.

“Ba za mu zauna da ’yan ta’adda ba, ba za mu yi sassanci da ’yan ta’adda ba, amma idan dan ta’adda ya ji wuta ya zo ya ce mana ya yarda zai ajaye makamansa sai mu amshe shi sannan ya shigo cikin mutane.” (Garba Abdullahi Bagwai)