logo

HAUSA

Sin na matukar adawa da Amurka ta danne kamfanoninta ba tare da wani dalili ba

2024-02-01 20:04:56 CMG Hausa

Ma’ikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi martani ga sabon bayanin “jerin kamfanonin sojan kasar Sin” da ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar a taron manema labarai na yau, inda kakakin ma'aikatar Wang Wenbin ya bayyana cewa, muna matukar adawa da yadda Amurka ta yi wa kasashe kudin goro a cikin tsarin tsaron kasarta, da zakulo jerin sunaye da nufin nuna wariya ga bangarori daban-daban, da kuma danne kamfanonin kasar Sin, da durkushewar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na yau da kullum tsakanin Sin da Amurka.

A martaninsa game da abin da ake kira "Masu kutse ta internet na kasar Sin", Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin na adawa da kuma murkushe bisa ga doka duk wani nau'i na kai hari ta yanar gizo. Amurka ta yi gaggawar yanke hukunci ba tare da ingantacciyar shaida ba, tana zargi da bata wa kasar Sin suna ba gaira ba dalili, wanda hakan bai dace ba, tare da kawo rudani tsakanin daidai da rashin daidai. Kasar Sin tana adawa da hakan. (Yahaya)