logo

HAUSA

CMG ta yi bayani kan shirye-shirye da kirkire-kirkiren fasaha a liyafar bikin bazara ta 2024

2024-02-01 19:57:52 CMG HAUSA

 

Yau Alhamis, CMG ta kira taron manema labarai kan liyafar bikin bazara wato bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta Loong ta shekarar 2024, don bayyana shirye-shirye da za a gabatar a bikin, da kuma sabbin kirkire-kirkiren fasaha da za a yi amfani da su a bikin.

Bisa labarin da aka bayar, an hada nagartattun al’adun gargajiya da salon fasaha na zamani a cikin bikin a wannan karo.

An ce, CGTN dake karkashin CMG zai watsa wannan kasaitaccen biki ga duk fadin duniya a cikin harsuna 68, inda kuma za a yi hadin kai da kafofin yada labarai fiye da 1500 na kasashe ko yankuna sama da 200 don watsa wannan biki kai tsaye. (Amina Xu)