logo

HAUSA

Kamaru za ta yi yaki da cin hanci da rashawa don inganta tattalin arzikin kasar

2024-02-01 14:09:32 CMG Hausa

Kasar Kamaru za ta kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa, domin taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta kasar (CONAC) Dieudonne Massi Gams, ya shaidawa manema labarai cewa, za su gudanar da bincike na zahiri don gano shaida ko zargin da aka gabatarwa hukumar. Don haka, shekarar 2024 za ta kasance shekara mai muhimmancin gaske wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa, kasar Kamaru na son zama kasar da za ta kakkabe matsalar cin hanci da rashawa, kuma ya kamata 'yan kasar su hada kai da hukumar CONAC, domin yaki da cin hanci da rashawa a dukkan fannoni.(Ibrahim)