logo

HAUSA

Ministar wajen Afirka ta Kudu: Kasashe biyar sun zama mambobin BRICS a hukumance

2024-02-01 19:10:49 CMG Hausa

 

A ranar 31 ga watan Janairu, ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta sanar da cewa, an tabbatar da kasashen Masar, Habasha, Iran, Saudi Arabiya, da Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin mambobin kungiyar ta BRICS a hukumance. A halin yanzu, adadin kasashe mambobin BRICS ya karu daga 5 zuwa 10. (Yahaya)