logo

HAUSA

Sin: Taimakawa lardin Hunan don habaka hadin gwiwa da Afirka

2024-01-31 20:21:36 CMG Hausa

Kwanan baya ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da cikakken shirin gina yankin gwaji na zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka a hukumance. A gun taron manema labarai na musamman na yau, jami’an ma’aikatar kasuwancin kasar Sin sun bayyana cewa, kasar Sin za ta kara inganta hada-hadar albarkatu, ta hanyar yin amfani da damar masana’antu da yankunan lardin Hunan, da kuma goyon bayan saurin bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.

An ba da rahoton cewa, cikakken shirin gina yankin gwaji don zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka, ya ba da shawara game da abubuwan da ake bukata a bayyane. Ya kamata yankin na gwaji ya maida hankali kan gina yankin kirkire-kirkire na hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tare da Afirka, yankin da ke kan gaba wajen zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tare da Afirka, da yankin da ke yin hadin gwiwar tsarin masana'antu da Afirka, da "dakin karbar baki" na hadin gwiwar tattalin arziki da mu'amalar cinikayya da Afirka. Har ila yau, ya kamata a gina cibiyar rarraba kayayyakin amfanin gona da ba ta Afirka ba, da cibiyar hadin gwiwar cinikayya ta yanar gizo ta kasar Sin da Afirka, da cibiyar inganta tsarin masana'antu ta kasar Sin da Afirka, da cibiyar hadin gwiwar hada-hadar kudi ta kasar Sin da Afirka, da cibiyar jigilar kayayyaki zuwa Afirka dake yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin, da kuma wata cibiya ta inganta cudanyar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka. (Yahaya)