logo

HAUSA

Kasashen duniya na yin kira da a gudanar da taron wanzar da zaman lafiya kan rikicin Palasdinu da Isra’ila

2024-01-31 21:00:57 CMG HAUSA

Yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jagoranci taron manema labarai, inda ya amsa tambayar da aka masa game da ra’ayin Sin kan batun gudanar da taron tattauna kan batun samar da zaman lafiya a Palasdinu.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, Xi Jinping sau da dama ya bayyana matsayin Sin wajen warware rikicin Palasdinu wato kira taron shimfidar zaman lafiya. Bayan barkewar rikici a wannan karo, Sin ta gabatarwa kwamitin sulhu na MDD takardar ra’ayin Sin game da warware rikicin Palasdinu da Isr’aila, inda ta sake yin kira da a gudanar da taro ba tare da bata lokaci ba. Ra’ayin kuma ya samun amincewa daga kasa da kasa.

Game da aya mai lamba 23 na babbar dokar yankin Hong Kong da aka sanar da fara aiwatarwa, Wang Wenbin ya yi tsokaci cewa, kafa wannan doka nauyin ne dake wuyan gwamnatin musamman na yankin wajen tabbatar da tsaron kasar a bangaren tsarin mulki, kana abin da ya zama dole ne a yi wajen tabbatar da kudurorin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin game da babbar dokar yankin Hong Kong da dokar tabbatar da tsaron yankin.

Yayin da ya tabo maganar matakan da Amurka ta kan dauka wajen yiwa daliban Sin da suka je Amurka karatu takala ba gaira ba dalili bisa burin siyasa, ya ce, matakan da ‘yan sandan Amurka suka dauka na keta hakkin wadannan dalibai, kasar Sin na nuna matukar rashin jin dadi ga bangaren Amurka. (Amina Xu)