logo

HAUSA

Kamata Ya Yi Amurka Ta Yi Dogaro Da Kanta Don Warware Matsalar Miyagun Kwayoyi

2024-01-31 22:08:47 CMG HAUSA

Ran 30 ga wata, an sanar da kaddamar da rukunin hadin kan Sin da Amurka wajen magance matsalar miyagun kwayoyi. Wanda ya zama wani muhimmin mataki wajen tabbatar da matsayan shugabannin kasashen biyu a ganawarsu a birnin San Francisco.

Da ma a watan Agusta na shekarar 2022, tsohuwar kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kai ziyara yankin Taiwan na kasar Sin, matakin da ya sabawa ka’idar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, lamarin da ya sa Sin ta dakatar da hadin kan ta da Amurka wajen magance matsalar miyagun kwayoyi. A wannan karo kuma, hukumomin yaki da miyagun kwayoyin kasashen biyu sun fara aiwatar da tsarin shawarwari da hadin kai, abin da ya bayyana kyautatuwar halin mu’ammala tsakaninsu, wanda kuma ya taka rawa wajen ingiza huldar kasashen biyu.

Amma abin lura shi ne, a matsayin kasa da ta fi fuskantar matsalar miyagun kwayoyi nau’in Fentanyl, har ila yau, Amurka ba ta fitar da matakin da ya dace don hana yin amfani da irin wannan sinadari mai guba ba. Saboda haka, ko da yake hadin kan tsakanin kasashen biyu na iya taimakawa Amurka wajen kyautata wasu harkoki, amma dole ne Amurka ta binciki kanta don gano ainihin dalilin da ya haifar da matsala, da dogaro da kanta wajen daidaita matsalar miyagun kwayoyi daga tushe. (Amina Xu)