logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Shugaban Babban Zauren MDD

2024-01-31 13:40:42 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da shugaban babban zauren MDD na 78 Dennis Francis, jiya Talata a nan birnin Beijing.

Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce kasar Sin na matukar goyon bayan hulda da cudanyar bangarori daban daban, haka kuma ta kasance mai ba da kariya ga ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin za ta goyi bayan rawar da MDD ke takawa a tsarin jagorantar harkokin duniya da ma muhimmiyar rawar da babban zauren majalisar ke takawa bisa ka’idojin majalisar.

Da ya tabo batun taro kan makomar duniya da majalisar za ta gudanar a watan Satumba, Wang Yi ya ce, Sin na fatan taron zai lalubo mafita ga kalubalen da duniya ke fuskanta.

A nasa bangare, Dennis Francis ya ce, har kullum, MDD na biyayya ga manufar Sin daya tak a duniya. Ya ce majalisar na yabawa dadadden goyon bayan da Sin ke bayarwa ga huldar kasa da kasa da hada hannu da ita, haka kuma tana jinjinawa muhimman shawarwari da shirye-shiryen da Sin ke gabatarwa. (Fa’iza Mustapha)