logo

HAUSA

MDD ta kaddamar da shirin jin kai na dalar Amurka biliyan 1.6 a Somalia

2024-01-31 09:51:21 CMG Hausa

 

MDD ta kaddamar da wani shirin ba da agajin jin kai na shekarar 2024, wanda ke bukatar dalar Amurka biliyan 1.6 domin taimakawa mutanen kasar Somalia miliyan 5.2 mabukata.

Kakakin sakatare janar na MDD Stephane Dujarric, ya bayyana jiya yayin taron manema labarai da aka saba yi cewa, majalisar ta gabatar da shirin ne tare da hadin gwiwar abokan huldarta da gwamnatocin jihohi da na kasar Somalia.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA) ya yi gargadin cewa, mutane sama da miliyan 4, wato kusan kashi 1 bisa kashi 4 na al’ummar kasar na cikin matsananciyar matsalar rashin abinci.

Alkaluman masu tayar da hankali sun kuma nuna cewa, 2 daga cikin kowanne yara 5 da shekarunsu bai kai 5 ba, na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki. Haka kuma, kasar na fama da matukar matsalar ‘yan gudun hijira, inda kimanin daidaikun mutane miliyan 3.8 suka rasa matsugunansu saboda matsaloli daban daban.

Har ila yau, ban da mummunar matsalar jin kai, yanzu Somalia na fuskantar barkewar cutar amai da gudawa, wadda ke yaduwa cikin sauri a yankuna daban daban dake kasar. (Fa’iza Mustapha)