logo

HAUSA

Xi ya jagoranci taron shugabannin JKS domin duba rahotanni da ka’idoji

2024-01-31 19:12:24 CMG Hausa

A yau Laraba ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS.

Taron ya yi nazari kan rahoton zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, bayan da ya saurari tare da tattauna rahotannin ayyukan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalisar gudanawar kasar, da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da kotun kolin jama’a, da hukumar kolin gabatar da kararrakin jama’ar kasar, da rahoton ayyukan sakatariyar kwamitn kolin JKS. (Yahaya)