logo

HAUSA

Xinjiang ta samu bunkasuwar yawon bude ido a 2023

2024-01-31 19:25:04 CMG Hausa

A shekarar 2023, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin ta karbi masu yawon bude ido miliyan 265, adadin da ya karu da kashi 117 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, adadin kudaden shigar yawon bude ido ya kai kusan yuan biliyan 296.72 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 41.77, wanda ya karu da kashi 227 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2022.

Adadin fasinjojin da suka yi zirga-zirga a filayen tashi da saukar jiragen sama na yankin ya zarce miliyan 40 a karon farko a bara, wanda ya karu da kashi 143.8 idan aka kwatanta da na shekarar 2022.

Alkaluman da aka bayyana a cikin rahoton ayyukan gwamnatin yankin yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar jihar Xinjiang, wanda aka bude ranar Talata, ya nuna irin gagarumin ci gaban yawon bude ido a jihar Xinjiang da kuma rawar da yawon bude ido ke takawa wajen fadada ayyukan yi, da bunkasa sayayya da kuma inganta rayuwar al'ummar yankin. (Yahaya)