logo

HAUSA

Bahar:Nasarorin da Sin ta cimma a fannin makamashi mai tsafta abin misali ne ga daukacin duniya

2024-01-30 10:36:57 CMG Hausa

Babban manazarci a hukumar kula da makamashi ta duniya (IEA) Heymi Bahar ya bayyana cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin makamashin da ake iya sabuntawa, abin misali ne ga daukacin duniya.

A cikin rahoton shekara-shekara da hukumar IEA ta fitar a farkon wannan watan, ta lura cewa duniya ta samu karin kashi 50 cikin 100 na karfin makamashin da ake iya sabuntawa a cikin shekarar 2023, fiye da na shekarar 2022, inda ta yi hasashen za a samu saurin bunkasuwa a shekaru biyar masu zuwa.

Bahar ya kara da cewa, ci gaban da aka samu a fannin samar da wutar lantarki bisa hasken rana, kasar Sin ita kadai ta girka kusan na’urorin samar da wutar lantarki bisa haske da suka kai karfin 220GW, daidai da sauran kasashen duniya, wanda ya ninka saurinta a cikin shekara guda.

Bahar, daya daga cikin mawallafin rahoton hukumar ta IEA, ya bayyana a wata hira da jaridar South China Morning Post cewa, kasar Sin ta yi fice a matsayin kasar da ta fi kowace kasa a duniya samar da na'urorin samar da wutar lantarki bisa hasken rana na PV a duniya, inda ta ba da gudummawar kusan kashi 80 cikin 100 na masana'antun dake samar da irin wadannan na’urori a duniya. (Ibrahm Yaya)