logo

HAUSA

Gidauniyar tallafawa kasashe masu rauni ta kasar Qatar ta kaddamar da wasu ayyuka a birnin Maiduguri ta jihar Borno

2024-01-30 09:19:30 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya jagoranci bikin kaddamar da wasu manya ayyukan jin kai guda 8 da gidauniyar tallafawa masu karamin karfi ta kasar Qatar ta dauki nauyin gudanarwa a birnin Maiduguri ta jihar Borno a arewa masu gabashin Najeriya.

Ayyukan da aka kadamar dai sun kunshi gidan marayu da makaranta da asibiti da gidan malamai da filin wasanni da ofishin jami’an jin kai da masallacin Juma’a da kuma shagunan sayayya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake jawabi, gwamnan na jihar Borno ya bayyana godiyarsa ne bisa yadda wannan gidauniya ta zabi jihar a matsayin daya daga cikin jihohin da za su amfana da ayyukanta a tarayyar Najeriya, ayyukan da kamar yadda ya ce suna da tasiri na kai tsaye ga rayuwar al’umma.

“Muna da adadin yara marayu sama da dubu 100 a jihar Borno sakamakon rikicin Boko Haram, wannan kiyasi ne na hukuma, amma adadin zai iya haura hakan a lissafin da ba na gwamnati ba. A shekaru 7 zuwa 8 da suka gabata, kusan mutane miliyan 3.2 ne suka rasa muhallan su, wanda yanzu haka an samu nasarar sake tsugunnar da kaso 50 na wadannan mutane, yayin da kuma kusan miliyan 1.2 kuma yanzu haka suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira daban daban dake jihar. Ha’ila yau cibiyoyin kiwon lafiya guda 432 ne aka lalata, an rusa gidaje dubu 900 da kuma  azuzuwan karatun dubu 5 duk sakamakon rikicin na Boko Haram.” 

A nasa jawabin, wakilin gidauniyarta kasar Qatar Hamdin Bin-Abdul cewa ya yi, “Mun ji dadi sosai bisa yadda gwamna ya baiwa wannan gidauniya tamu damar hada kai da gwamnatin jihar domin yin hidima ga ’yan uwa da abokan arziki dake jihar ta Borno. (Garba Abdullahi Bagwai)