logo

HAUSA

Binciken kwatsam da Amurka ta yi kan kamfanin Sin ya janyo sanyin gwiwa game da kasuwar Amurka

2024-01-30 19:37:35 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a yau Talata cewa, binciken kwatsam da Amurka ta yi a kan wani kamfanin kasar Sin ya sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasar game da yin kasuwanci a Amurka.

Binciken ba zato ba tsammani da aka gudanar a kan Sinawa mazauna Amurka, tare da kwace musu wayoyin salula da kwamfutoci da sauran na’urorinsu, ya kawo cikas ga harkokin yau da kullun na kamfanoni da ‘yan kasuwa na kasar Sin, a cewar kakakin yayin da yake mayar da martani kan batun.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata bangaren Amurka ya daina tsangwamar da yake yi nan da nan, tare da tabbatar da samar da yanayin kasuwanci mai aminci, gaskiya da adalci ga kamfanoni da 'yan kasuwa na kasar Sin. (Yahaya)