logo

HAUSA

Sin ta yi kakkausar suka ga nuna "munafurci" wajen yaki da ta'addanci

2024-01-30 20:46:04 CMG Hausa

A ranar 30 ga watan Janairu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jagoranci taron manema labarai da aka saba yi. Wani dan jarida ya yi tambaya game da zargin da Pakistan ta yi na cewa jami'an leken asirin Indiya na da hannu a kisan 'yan Pakistan a Pakistan. Wang Wenbin ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya lura da rahotannin da abin ya shafa. Ya jaddada cewa, ta'addanci makiyin bil'adama ne. Kasar Sin ta yi kakkausar suka ga nuna “munafurci" kan batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci, wadanda ke cutar da sauran jama'a. Kasar Sin a shirye take ta karfafa hadin gwiwar yaki da ta'addanci tare da sauran kasashe, domn yaki da duk wani nau'in ta'addanci.

Game da tattaunawar da Rasha ke ci gaba da yi da sauran kasashen BRICS kan huldar tsarin sadar da bayanan hada-hadar kudi na kasa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kiyaye daidaiton harkokin kudi na duniya, da kyautata tsarin tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya, wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi na kasa da kasa, wadanda ke da alaka da moriyar bai daya ta dukkan kasashen duniya. Kasar Sin tana goyon bayan kokarin da ake yi ta hanyoyin da suka dace, kuma a shirye take ta taka nata rawar wajen kyautata tsarin tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya. (Yahaya)