logo

HAUSA

Sin: Taya Azali murnar sake zabarsa a matsayin shugaban Comoros

2024-01-29 20:12:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jagoranci taron manema labarai a ranar 29 ga watan Janairu. Yayin da yake tattaunawa kan sakamakon zaben shugaban kasar Comoros, ya ce kasar Sin tana taya Mista Azali Assoumani murnar sake lashe zabe a matsayin shugaban kasar Comoros.

Dangane da halin da ake ciki na kwanan nan, na nazari kan hakkin bil Adama na kasa na kwamitin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Wang Wenbin ya ce, taron kwamitin kula da hakkin bil Adama na MDD karo na 45 kan nazarin hakkin bil Adama na kasa, ya amince da rahoton kasar Sin a zagaye na hudu na bitar hakkin bil Adama na kasa. Sama da kasashe 120 ne suka yi nazari sosai kan ci gaban da aka samu a fannin kare hakkin dan Adam na kasar Sin, tare da tabbatar da cikakken kokarin kasar Sin na ci gaba da kare hakkin dan Adam.

Game da dangantakar tattalin arziki da cinikayyar tsakanin Sin da Amurka, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kiyaye bunkasuwar dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ya kasance moriyar kasashen biyu da jama'arsu.

Dangane da matakan wucin gadi da kotun duniya ta MDD ko ICJ ta dauka kan zirin Gaza, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin na fatan za a aiwatar da matakan wucin gadi na ICJ yadda ya kamata. (Yahaya)