logo

HAUSA

An daga tutar kasar Sin a Nauru, bayan kusan shekaru 19 da dakatar da dangantaka

2024-01-29 14:27:29 CMG Hausa

A yau Litinin, tawagar jami’an diplomasiyya ta kasar Sin, ta yi bikin daga tutar kasar Sin a Nauru, karon farko cikin kusan shekaru 19 da aka daga jar tutar mai taurari 5 a tsibirin dake yankin Pasifik.

Jami’an da aka dorawa alhakin farfado da ofishin jakadancin Sin a Nauru ne suka gudanar da bikin a harabar dake dauke da ofisoshinsu na wucin gadi.

Shugaban tawagar jami’an diplomasiyya na kasar Sin Wang Xuguang, ya shaidawa manema labarai cewa, dangantakar kasashen Sin da Nauru na dauke da dimbin damarmaki.

A ranar 15 ga watan Junairu ne gwamnatin kasar Nauru ta sanar da cewa, ta amince da manufar Sin daya tak a duniya, kana ta katse hulda da hukumomin yankin Taiwan, haka kuma ta shirya dawo da huldar diplomaisyya da kasar Sin.

A kuma ranar 24 ga wata ne a nan birnin Beijing, kasashen Sin da Nauru suka rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwa, wadda ta sanar da dawo da huldar diplomasiyya a tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)