logo

HAUSA

ECOWAS ta ce har yanzu kasashen yammacin Afirka uku mambobinta ne

2024-01-29 10:12:00 CMG Hausa

Kungiyar ECOWAS ta sanar a jiya Lahadi cewa, Burkina Faso da Nijer da Mali mambobinta ne da ba za a iya raba su da kungiyar ba. Wannan na zuwa ne a matsayin martaninta ga wata sanarwar da kasashen uku suka fitar tare, ta janyewa daga kungiyar.  

A cikin sanarwar da ta fitar, ECOWAS ta ce, har yanzu ba ta samu sanarwa ta kai tsaye dake cewa kasashen uku sun janye daga kungiyar ba.

Kasashen Burkina Faso da Nijer da Mali, mambobi ne masu muhimmanci na kungiyar ECOWAS a halin yanzu, kuma shugabannin kasashen da gwamnatocinsu sun himmatu wajen warware mawuyacin halin siyasa da suke ciki ta hanyar tattaunawa. (Safiyah Ma)