logo

HAUSA

Sin ta sha alwashin tallawafa masana'antun zamani

2024-01-29 21:30:18 CMG Hausa

Kasar Sin za ta ba da goyon baya ga sabbin fasahohi, da harkokin samar da masana’antu da gudanar da harkoki na tsaro na masana'antu da za a samar a nan gaba, a cewar ka'idar gwamnati.

Ya kamata a gina yankunan gwaji da rukunin ayyukan samar da masana’antu na nan gaba ya zuwa shekarar 2025, yayin da ya kamata a cimma nasarori a cikin muhimman fasahohi kusan dari a muhimman fannoni, bisa ga ka'idar da ma'aikatar masana'antu da sadarwa da wasu ma'aikatu da hukumomi shida suka fitar. (Yahaya)