logo

HAUSA

Masana’antun kauyukan Sin sun samu ci gaba yadda ya kamata a shekarar 2023

2024-01-28 15:51:55 CMG Hausa

Sabbin alkaluman da ma’aikatar kula da aikin gona da kauyuka ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, masana’antun kauyukan kasar sun samu ci gaba yadda ya kamata a shekarar 2023 da ta gabata.

Alal misali, sana’ar gyara kayayyakin aikin gona ta samu ci gaba cikin sauri, kuma adadin manyan kamfanonin gudanar da sana’ar a fadin kasar ya kai sama da dubu 90.

A sa’i daya kuma, an kafa sabbin yankunan aikin gona na zamani 50, da rukunonin masana’antu masu siffar musamman 40, da garuruwan masana’antun aikin gona masu karfi 200, da yankunan gwaji na aikin gona na zamani 100 a fadin kasar.

Haka zalika, ana kokarin raya sana’ar yawon shakatawa, da cinikayya ta yanar gizo a kauyuka.

Duk wadannan sun sa kudin shigar manoman kasar Sin ya karu, har karuwarsa ta kai kaso 7.6 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2022. (Jamila)