logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Plato: ayyukan dillalan kwayoyi ne babban dalilin da yake haifar da rashin zaman lafiya a jihar

2024-01-28 15:21:10 CMG HAUSA

 

Gwamnan jihar Plato dake arewa ta tsakiyar Najeriya Mr. Caleb Mutfwang ya alakanta yawan tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan jihar bisa ayyukan dillalan kwayoyi da suke sauya tunanin matasa wajen ta da zaune tsaye.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga wasu al’umomin da rikicin baya-bayan nan ya ritsa da su a yankin karamar hukumar Mangu, inda ya ce, bayan yaki da bijirarrun matasa haka kuma gwamnati za ta yi fito na fito da masu sana’ar sayar da haramtattun kwayoyi a fadin jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.