logo

HAUSA

Bankunan kasashen ketare sun yaba da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin

2024-01-28 15:39:10 CMG Hausa

Yayin da kasar Sin ta fitar da bayanai kan ci gaba tattalin arzikinta a shekarar 2023, kwararru daga cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje sun yi tsokaci mai kyau kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Jimillar bayanan tattalin arzikin sun kyautatu fiye da yadda aka yi tsammani tun daga watan Agusta, a cewar Zhu Haibin, babban masanin tattalin arzikin kasar Sin a J.P Morgan.

A bara, jimillar GDPn kasar Sin ya karu da kashi 5.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar da ta gabata, zuwa sabon matsayi da ya kai yuan triliyan 126.06 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 17.74, a cewar hukumar kididdiga ta kasar. Adadin ci gaba ya zarce hasashen gwamnati na samun ci gaban kusan kashi 5 cikin dari a duk shekara, kuma ya zarce karuwar kashi 3 cikin dari a 2022.

Xiong Yi, babban masanin tattalin arziki na kasar Sin a bankin Deutsche ya ce, "Rawar ganin masana'antun sarrafawa na kasar Sin suka taka a kasuwannin duniya na ci gaba da karuwa, kuma hade da fitar da kayayyaki masu fasahar sabbin makamashi guda uku zuwa kasashen waje ya kai darajar Yuan tiriliyan daya a karon farko, lamarin da ya ingiza sabon ci gaban tattalin arziki,"

Jimillar darajar fitar da kayayyakin masu fasahar sabbin makamashi guda uku na kasar Sin, wato batura masu amfani da hasken rana, da batirin lithium-ion da motocin lantarki, ta karu da kashi 29.9 cikin dari zuwa yuan tiriliyan 1.06 a shekarar 2023. (Yahaya)