logo

HAUSA

Majalisar Kare Hakkokin Bil Adama Ta Duniya Ta Amince Da Shawarwarin Kasar Sin

2024-01-27 15:22:25 CMG Hausa

Kwamitin nazarin yanayin kare hakkokin bil Adama a kasa da kasa na majalisar kula da hakkokin bil Adama ta duniya karo na 45, ya amince da shawarwarin da kasar Sin ta gabatar a jiya Jumma’a. Kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka shiga zagaye na 4 na nazarin da aka yi a wannan mako.

Chen Xu, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD a Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa da ke Switzerland ya ce, a shirye Sin take ta hada hannu da kasashen duniya wajen ingantawa da kare hakkokin bil Adama.

A cewarsa, kasar Sin za ta taka rawa wajen jagorantar ayyukan kare hakkokin bil Adama a duniya da daukaka darajar bil Adama ta bai daya da mara baya ga samun al’umma mai makoma ta bai daya da kuma hada hannu domin inganta yanayin duniya.

Yayin da a bana ake cika shekaru 75 da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, ya ce kasarsa na da niyyar tabbatar da ganin al’ummarta sun ci moriyar zamanantar da kasar bisa yanayi na adalci, da inganta kare hakkokin bil Adama da mara baya ga raya harkokin daidaikun mutane. (Fa’iza Mustapha)