logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Nauru: dawo da huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Nauru muhimmin lokaci ne a tarihi

2024-01-27 16:09:32 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Nauru Lionel Rouwen Aingimea ya ce sanarwar da Sin da Nauru suka yi na dawo da huldar diplomasiyya a tsakaninsu, wani muhimmin lokaci ne a tarihi, wanda zai sa kaimi ga kasar Nauru ta kara samun ci gaba.

Ministan ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a baya-bayan nan, yana mai cewa, dawo da huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Nauru da amincewa da ka’idar Sin daya tak a duniya, muhimmin kuduri ne da kasar Nauru ta tsai da bayan ta yi nazari sosai. Kuma kasar za ta ci gaba da hada hannu da kasar Sin a nan gaba.

Game da ka’idar kasancewar Sin daya tak a duniya, minista Aingimea ya bayyana cewa, kiyaye ka’idar tushe ne na aiwatar da ayyukan dake shafar kasar Sin. Ya ce ko da yake an dawo da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu ba da dadewa ba, amma yadda Sin ta dauki Nauru da muhimmanci, tamkar yadda kasashen biyu tsofaffin abokai ne, ba na tsawon shekaru 10 ko 20 kadai ba, kamar na shekaru 100 ko 200. (Zainab Zhang)