logo

HAUSA

Najeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyarta da MDD wajen kawo karshen shigar kananan yara ayyukan ta’addanci

2024-01-27 15:05:03 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniya tsakaninta da majalissar dinkin duniya wajen tabbatar da ganin an kare tare da sakin kananan yaran da jami’an tsaro suka kama yayin hare-haren ta’addanci a kasar da kuma yankin tafkin Chadi.

Wannan mataki yana daya daga cikin tsare-tsaren da ake yi wajen ganin an dawo da irin wadannan kananan yara cikin al’umma domin ci gaba da gudanar da rayuwa, wanda yanzu haka suke a tsare karkashin kulawar gwamnati.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

An dai zartas da wannan yarjejeniya ce a birnin Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki da suka hada da hukumomin tsaron Najeriya, da ma’aikatar mata da wakilan majalissar dinkin duniya da kuma na hukumar UNICEF.

Alkaluma daga hedikwatar tsaron Najeriya dai sun nuna cewa, kananan yara da dama ne ’yan ta’adda suka kama a Najeriya kuma suka tilasta musu shiga ayyukan ta’addanci, yayin da kuma wadanda aka haifa a sansanonin ’yan ta’addan aka sauya musu tunani zuwa na ta’addanci.

Rear Admiral Yaminu Musa shi ne jami’in dake lura da cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci dake karkashin ofishin mashawarcin shugaban Najeriya kan sha’anin tsaro.

“Yarjejeniyar fitar da kananan yaran tsari ne dake da nufin hanawa ko kuma rage yawan yaran da ake tsare da su a sakamakon fito na fito da sojoji da sauran jami’an tsaro suka yi da ’yan ta’adda, tare da mika irin wadannan yara da ake zargin suna da alaka da kungiyoyin ’yan ta’adda ga ma’aikatar mata.”

Wakilin rundunar sojin Najeriya a wajen taron Major Janaral Nosakhare Ugbo cewa ya yi, “Rundunar sojin Najeriya za ta tabbatar da ganin cewa dukkan jami’anta sun kiyaye tare da aiwatar da abubuwan dake kunshe cikin wannan yarjejeniya dake da bukatar kare kananan yaran da aka samu da hannu a ayyukan ta’addanci.” (Garba Abdullahi Bagwai)