logo

HAUSA

Li Qiang ya aika da wasikar taya murna ga sabon firaministan kasar Kuwait

2024-01-27 21:41:39 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya aika da wasika zuwa ga Sheikh Mohammad Sabah Al-Salem Al-Sabah, sabon firaministan kasar Kuwait don taya shi murnar kama wannan mukamin. Cikin wasikar da ya aika a jiya, Li Qiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na son hadin gwiwa da gwamnatin Kuwait wajen aiwatar da muhimman ra’ayoyi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa amincewar juna a siyasance, da inganta cudanya da hadin kan kasashen biyu a fannoni daban daban, gami da kara tuntubar juna kan lamuran shiyya-shiyya da na duniya.(Kande Gao)