logo

HAUSA

Shugaban Ghana Ya Kaddamar Da Sabuwar Matatar Man Fetur Da Sin Ta Gina A Kasar

2024-01-27 15:39:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kaddamar da kashin farko na matatar mai da kamfanin kasar Sin ya gina a birnin Tema mai gabar ruwa dake a kudancin kasar.

Ana sa ran matatar ta Sentuo, wadda wani kamfanin kasar Sin mai zaman kansa ya gina, za ta samar da dubban guraben ayyukan yi bayan kammala kashi na 2 na aikin.

Da yake jawabi ga jama’ar da suka halarci kaddamarwar a jiya Jumma’a, shugaba Akufo-Addo ya ce, amincewa da gina matatar a kasar, ya bayyana burin Ghana na tabbatar da tsayawa da kafarta a bangaren makamashi a nan gaba. Ya kuma jaddada cewa, kafa matatar, wata alama ce ta dadaddiyar dangantakar dake tsakanin Ghana da kasar Sin.

Da yake jawabi, jakadan kasar Sin a Ghana Lu Kun, ya bayyana cewa, kaddamar da matatar ta nuna kudurin ‘yan kasuwar kasar Sin na ci gaba da zuba jari a Ghana domin bunkasa tattalin arzikin kasar, yana mai nanata cewa, Sin da Ghana sun raya dangantaka mai karfi kuma ta kut-da-kut a tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)