logo

HAUSA

CMG na Sin da gidan telebijin na BFM na Faransa sun gabatar da shirin musamman na yin hira da manyan jami’an gwamnati

2024-01-27 16:14:21 CMG Hausa

A yau Asabar, babban rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da gidan telebijin na tattalin arziki na BFM na kasar Faransa, sun gabatar da shirin musamman na hira da manyan jami’an gwamnati mai taken “hira da manyan jami’ai don murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Faransa”.

Tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin ya bayyana a cikin shirin cewa, an mayar da hankali wajen samun sabon ci gaban hadin gwiwa tsakanin Faransan da Sin, wanda ke da muhimmanci sosai wajen kara mu’amala da juna. Ya ce shekaru 60 da suka gabata, janar Charles André Joseph Marie de Gaulle ya tsai da kudurin kulla huldar diplomasiyya tsakanin Faransa da Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. Kuma a halin yanzu, Faransa tana fatan duk duniya za ta gane cewa ana bukatar kasar Sin wajen kiyaye zaman lafiya a duniya. Ya kara da cewa, Sin kasa ce dake da al’adu daban daban, kana kowane birnin kasar yana da alamarsa ta musamman, yana mai cewa, idan ana son fahimtar kasar Sin, to sai a ziyarci kasar. (Zainab Zhang)