logo

HAUSA

Ana Sa Ran Samun Tafiye-tafiye Miliyan 182 A Rana Ta Farko Na Fara Bulaguro Domin Bikin Bazara

2024-01-26 20:36:58 CMG Hausa

Ana sa ran samun tafiye-tafiye sama da miliyan 182 a yau Jumma’a, rana ta farko na kwanaki 40 da za a shafe ana tafiye-tafiye domin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.

Bisa hasashen kwamitin aiki na musammam da ya kunshi sassan gwamnati da dama da suka hada da ma’aikatar sufuri da ma’aikatar kula da tsaron al’umma da kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen kasa, daga cikin jimilar adadin, za a yi tafiye-tafiye miliyan 10.6 ta jirgin kasa, sai miliyan 170 da za a yi kan manyan tituna.

Kwamitin ya kuma yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen da za a yi ta ruwa zai kai 520,000, yayin da na sama zai kai sama da miliyan 2 a yau Jumma’a.

Lokacin wanda ake kira da ‘Chunyun’ zai shaida ganin miliyoyin al’umma na komawa garuruwansu domin haduwa da ‘yan uwa da abokan arziki.

Hutun Bikin Bazara wato sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin a bana, zai fara ne daga ranar 10 zuwa 17 ga watan Fabrairu, inda aka samu karin kwana guda kan na shekarun baya. (Fa’iza Mustapha)