Maido da huldar diflomasiya tsakanin Sin da Nauru ya sake tabbatar da matsaya guda uku da kasashen duniya suka cimma
2024-01-26 13:50:21 CMG Hausa
Kwanan nan, al’ummun kasar Nauru dake tsibirin tekun Pasifik sun yi maraba da maido da huldar diflomasiya tsakanin Nauru da Sin. Kafin wannan, majalisar Nauru ta zartas da kudurin katse hulda tsakanin Nauru da yankin Taiwan na kasar Sin tare da maido da huldar diflomasiya da Sin.
Nauru ta maido da huldar diplomasiya tsakaninta da Sin ba tare da wani sharadi ba, wanda ya kasance shawarar diplomasiya da ta yanke da kanta, kuma ya sake tabbatar da cewa, ka'idar kasancewar Sin daya tak a duniya, ita ce matsayar da kasashen duniya suke dauka .
Sin da Nauru sun maido da huldar diplomasiya, wanda ya kori kalaman wai nuna adawa da kudurin MDD mai lamba 2758. Gwamnatin Nauru ta bayanna a cikin sanarwar da ta fitar cewa, bisa kudurin MDD mai lamba 2758, ta amince cewa, gwamnatin jamhuriyyar jama’ar Sin ita ce halaltacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar Sin baki daya, kuma Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba.
Wannan ya tabbatar da cewa, kudurin MDD mai lamba 2758 dake tabbatar manufar kasar Sin daya tak, kuduri ne da kasa da kasa suka amince da shi, kuma babu wanda zai iya sauya shi.
Ban da wannan, maido da huldar diplomasiya tsakanin sassan biyu, ya sa duniya ta kara fahimtar cewa, “’yancin kan Taiwan” ba zai samu nasara ba. Tun lokacin da jam'iyyar Democrat a yankin Taiwan ta hau karagar mulki a shekarar 2016, kasashen duniya fiye da 10 sun katse huldar dake tsakaninsu da hukumomin yankin Taiwan.
Ministan kudi na kasar Tuvalu ya bayyana a yayin wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ana sa ran kasar Tuvalu za ta duba yiwuwar daidaita huldar tsakaninta da yankin Taiwan. Matakin “kulla huldar diplomasiya ta hanyar biyan kudi” da gwamnatin yankin Taiwan ta dauka ba zai yi amfani ba, kuma tana cikin hadari sosai, idan har tana son rike kasashe guda 12 da ake kira “kasashen dake huldar diplomasiya da yankin”. (Safiyah Ma)