logo

HAUSA

Shugaban Babban Taron MDD Na 78 Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

2024-01-26 21:31:56 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya yi masa, shugaban babban taron MDD na 78 Dennis Francis, zai ziyarci kasar Sin daga ranar gobe, 27 zuwa 31 ga watan nan na Janairu. (Fa’iza Mustapha)