logo

HAUSA

An kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na bana

2024-01-26 14:08:48 CMG Hausa

Yau Jumma’a, ita ce rana ta farko da aka fara kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na shekarar bana. An yi hasashen cewa, yawan fasinjojin da za a yi jigilarsu ta hanyar jiragen kasa a yau, zai kai miliyan 10.6.

A cikin kwanaki 40 masu zuwa yayin da aka kaddamar da zirga-zirgar, an yi hasashen cewa, yawan fasinjoji da za a yi jigilarsu ta hanyar jiragen kasa zai kai miliyan 480, matsakaicin yawan fasinjojin a kowace rana zai kai miliyan 12, kuma yawan zirga-zirgar fasinjoji da ake jigilarsu daga wani yanki zuwa wani daban, zai kai biliyan 9.

Zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na shekarar bana ita ce zirga-zirga ta farko bayan kawar da cutar numfashi ta COVID-19. An yi hasashen cewa, fasinjojin da ake jigilarsu ta hanyar jiragen kasa sun hada da masu ziyarar dangogi da dalibai da ma’aikata da kuma masu yawon bude ido. (Safiyah Ma)