logo

HAUSA

An yi hasashen tattalin arzikin Afirka zai karu da kashi 3.5 a shekarar 2024

2024-01-26 09:59:23 CMG Hausa

Rahoton MDD na shekarar 2024, game da halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, ya yi hasashen ci gaba da bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar Afirka a shekarar 2024, duk da tashe-tashen hankula a fannin siyasa, da matsalar yanayi da dorewar matsalar basussuka.

Da yake kaddamar da rahoton WESP na shekarar 2024 jiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, jami'in hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin Afirka (UNECA) Hopestone Chavula ya ce, ana hasashen ci gaban tattalin arzikin Afirka zai kasance mai sauki, wanda ya karu daga matsakaicin kashi 3.3 a shekarar 2023 zuwa kashi 3.5 cikin 100 a shekarar2024.

Ya ce, da dama daga cikin kasashen nahiyar, sun fuskanci hauhawar farashin kayayyaki a shekarar 2023, musamman saboda tsadar man fetur da abinci.

Chavula ya ce, tabarbarewar tattalin arzikin duniya, da tsauraran matakan harkoki da na kasafin kudi, da dorewar bashi mai yawa, za su ci gaba da zama matsalolin dake jan hankalin ci gaban yankin.(Ibrahim)