logo

HAUSA

Sama da mutane 30 ne suka mutu bayan barkewar wani sabon rikici a yankin Mangu ta jihar Plateau

2024-01-26 09:46:44 CMG Hausa

An sake samun barkewar wani rikici a yankin Kwahas-lakek dake karamar hukumar Mangun Jihar Plateau dake arewa ta tsakiyar Najeriya duk da dokar hana zurga-zurga da gwamnatin jihar ta kafa a ranar Lititin 22 ga wata a yankin.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya Alhamis, daraktan lura da harkokin kafofin labarai na hedikwatar tsaron Najeriya major-janaral Edward Buba ya ce, rikicin na baya-bayan nan ya faru ne bisa dalilai biyu, yunkurin satar shanu da kuma daukar fansa a kan kisan da aka yi wa mutumin da ake zargi da yunkurin satar shanun.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Major-janaral Edward Buba ya ce, tun farko dai a ranar Talata 23 ga wata, wani mutum dan kabilar Wangagu da yake kan babur ya nemi haikewa rukunin wasu shanu da suke kokarin ratsa titi, bayan dai sa’in sa a tsakaninsa da masu kula da shanun, daga bisani kuma suka halaka shi. A sakamakon hakan ne kuma wasu ’yan ta’adda suka yi gangami domin daukar fansa a kan masu kiwon shanu tare da afkawa gidajen jama’a dake yankin.

(Muryar Edward Buba)

Ya ce, tuni dai aka tura dakarun soji na musamman yankin da al`amari ya faru domin dai kashe wutar rikicin.

Haka kuma, major-janaral Edward Buba ya tabbatar da cewa, hedikwatar tsaro ta kasa za ta gana da shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen karamar hukumar ta Mangu Revd Timothy Daluk bayan furucin da ya yi na cewa, dakarun sojin da aka tura yankin domin tabbatar da zaman lafiya ba su aikin da ya kamata.

Sama dai mutane 30 ne aka kashe tare da kona gidaje yayin da wasu kuma da dama suka samu raunika a sabon rikicin da ya barke a kauye na Kwahas-lakek dake yankin karamar hukumar Mangu kwana guda da sanya dokar hana zurga-zurga da gwamnan jihar ya yi a yankin. (Garba Abdullahi Bagwai)