logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin zai ziyarci Thailand tare da tattaunawa da mashawarcin tsaro na Amurka

2024-01-26 11:15:09 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar Thailand, kuma ministan harkokin wajen kasar Parnpree Bahiddha-Nukara ya yi masa, ministan harkokin wajen kasar Sin, kana mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, Wang Yi, zai kai ziyara Thailand daga yau Jumma’a 26 zuwa 29 ga watan Janairu.

Haka kuma, bisa amincewar kasashen Sin da Amurka, Wang zai yi wani sabuwar tattaunawa da mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan a Bangkok. (Ibrahim Yaya)