logo

HAUSA

Faraministan kasar Nijar ya yi allawadai da halayyar kungiyar CEDEAO a yayin wani taron manema labarai a birnin Yamai

2024-01-26 10:51:19 CMG Hausa

A ranar jiya Alhamis 25 ga watan Janairun shekarar 2024, shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine ya kira wani taron manema labarai a fadarsa dake birnin Yamai. Makasudin wannan ganawa tare da ’yan jarida shi ne na ba su bayani kan ina aka kwana ina aka tashi game da tattaunawa tare da sabbin hukumomin Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Hakika a ranar jiya ne 25 ga watan Janairun shekarar 2024, Nijar da kungiyar CEDEAO ya kamata su fara tattaunawar da za ta taimaka ga janye takunkumin kasashen duniya tun bayan da sojoji suka karbe iko daga fararen hulla a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023. Haka zalika, batun sakin tsohon shugaban kasar Mohamed Bazoum da matarsa da ake ci gaba da tsare da su na kan teburin tattaunawar da ya kamata ta gudana a birnin Yamai.

Sai dai tagawar CEDEAO da ake dakon jiranta a ranar jiya, daga kamata ta taso daga Abujan Najeriya ba ta iso ba har zuwa yammacin ta ranar jiya 25 ga wata, in ji faraministan Nijar.

Gaban wannan rashin zuwan tawagar CEDEAO, faraminisan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine bai yi kasa a gwiwa ba, “An dauki alkawarin za’a tattaunawa da su rana ta yau, amma ba su zo ba. Muke jiransu tun da safe har bayan azahar, aka yi kiransu aka ce me ya sa ba ku samu zuwa ba, tun da an tura muku izinin zuwan duka bai wuce awa daya ba, sai muka samu labarin sun ce wai jirgin ne ya lalace, ba za su iyar zuwa ba. To wannan abu ne wanda yake rashin adalci da rashin gaskiya, al’ummar Nijar da al’ummar kasashen da suke cikin ECOWAS ya tsantsanta su sani, wannan kungiya ba ta bin gaskiya. Kuma an san kasashen da suke bayanta suke sa wa suna hanawa kuma a rashin gaskiya da rashin adalci da aka dorewa kasarmu duk da haka aka hakura, ake bin su don a zo a zauna amma sai dai mu ji a cikin rediyo suna suna jibga karya har kullum na cewa kasarsu ce basu yarda ba aje a tattauna a bisa haka.”

Sai dai a cikin wata sanarwar da kungiyar CEDEAO ta fitar a ranar jiya, ta shaidawa hukumomin Nijar cewa jirgin da ya kamata ya dauko tawagar CEDEAO daga birnin Abuja zuwa birnin Yamai ya lalace, dalilin ke nan aka jinkirta wannan zuwa.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.